Ingantaccen Karin karfin Maza mazakuta yana da matukar muhummanci ga maza, domin sautari maza kan samu matsalar biyawa iyalansu ...




A ranar Asabar ne wata likitar masu tabin hankali, Dr Maymuna Kadiri ta bai wa matan aure shawarar su dinga saduwa da mazajensu akai-akai domin su kare kansu daga ciwon damuwa sannan su sami farin ciki mara misaltuwa.

Kadiri, wadda take daraktar lafiya ta cibiyar "Pinnacle Medical Services" ta bayar da shawarar ga mata a wata tattaunawa da ta yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a jihar Legas.

Pinacle wata cibiyar lafiya ce da samar da zaman lafiya wadda take magance matsalolin da suka shafi lafiyar tunani, halayya da kuma kwakwalwar dan adam.

A dangane da jawabinta, ba wai don a dadadawa jikin mace kawai ake jima'i ba, yana ma da amfani ga lafiyar kwakwalwarta.

"A matsayinmu na mata, akwai bukatar mu mayar da mazajenmu aminanmu idan har muna so mu zama masu lafiyayyen tunani.
 
"Bincike ya nuna cewar matayen da suke yawaita jima'i da wadanda suka jima da aure basu kai matayen da ba sa jima'i fadawa matsalar ciwon damuwa ba.

"Saboda haka, yin jima'i da yawa na da amfani da mahimmanci. Magani ne da ke magance wa mata ciwon kai mai naci. 

"Yana da kyau a magance matsalar karancin sha'awa. Mace za ta iya samun kanta a cikin yanayin damuwa idan ta rasa karfin sha'awar da take da shi a baya. 

"Lafiyayyen jima'i akai-akai zai iya taka rawa gurin samar wa mace nutsuwa da ingancin rayuwa," Kadiri ta fada.

Ta yi jawabin cewa ba wai don a haifi 'ya'ya kawai ake jima'i ba, inda ta kara da fadin yana kara shakuwa, soyayya da kuma lafiyayyen barci.

Kadiri ta shawarci matan da ke fama da ciwon damuwa da su yawaita saduwa da mazajensu tare da inganta soyayyarsu.

Ta kuma shawarci matayen da suke da matukar kiba da suma su yawaita saduwa da mazajensu, inda ta ce yin hakan yana karfafa ingancin sinadarin "endorphins", wanda yake kula da farin ciki da annashuwa a jikin mutum.

"Sinadarin farin cikin zai sanya su rage teba sannan kuma su sami barci mai dadi.

"Inzali a lokacin jima'i yana sanyawa jiki ya samar da "endorphins" wanda sinadari ne na farin ciki da kwakwalwa take fitarwa, inda yake kawar da damuwa da radadi," inji ta.

Ta kara da fadar cewa jima'i ba ga maza kawai yake da amfani ba, su ma mata yana da mahimmanci gare su saboda yana iya ƙkawar masu da damuwa.
أحدث أقدم