Rarara yayi jawabin Daya sanya yayiwa Aishatul Humaira Waka........

Baka isa kace Aisha humairah ba mutumniyar kirki bace – Rarara





Shahararren mawakin siyasa a Nijeriya Adamu dauda Kahuta rarara ya hirar sa freedom radio kano inda ya fadi halaye da dabiu na jaruma aisha humaira maitamakiyarsa ko muce abokiyar aikinsa.


Rarara da aisha humairah akwai shakuwa sosai tsakaninsu shiyasa mutane suke masu kallon suna soyaya da dauda Kahuta rarara duba da har waka yayi mata ta soyayya yayi kalamai sosai a cikin wakarsa mai suna “Aisha”.
A tattaunawar rarara da freedom radio kano yana cewa

Mutane suna fasara da cewa aisha humairah ce kayiwa wannan waka mai suna Aisha me zakace ?

“To ai duk mai suna aisha sunanta humaira, wannan waka anyita ce akan fim ali nuhu ne da matarsa uwar gida Aisha, to zai yi mata kishiya ne, baima san zato zo wurin bikin ba domin anyi shine a munafuce, shine tazo tana shine yaga tayi fushi yake mata wannan waka, aisha kibar mani kuka aisha.

Rarara

Wannan waka ce da ankayi a cikin fim mai suna ‘A cikin biyu’ ba zance ne na zuciya ba, kuma alhamdullahi waka ta samu karbuwa domin duk wata mai suna aisha zata ji wakar sosai-inji rarara

Me zaka fadi abu biyu akan aisha ta zahiri?
Sai dai mutum yace maka baya son Aisha amma ba maganar cewa ba mutumniyar kirki bace,aisha bata da abokin fada idan ma kaga tana fada da mutum shine yayi mata laifi ba ita ba kuma zata yafe masa, duk wani furodusa ko darakta yayi aiki da aisha humairah sai yayi burin ta dawo wani aikinsa.”inji rarara

Sai dai in bai samu dama ba domin ita ba abun ya dame ta ba.-inji rarara.
أحدث أقدم