HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL!
Abokina Barr. Hamza Nuhu Dantani ✍️
Wato Labarin Yarinyar nan da wani mara imani yayi mata Fyade na da matukar tayar da Hankali duk cewa yanzu haka case din yana Gaban Kotu!
Wato a Zantawar da mukayi da iyayen yarinyar da kuma Shafa’atu wacca itace ta fara yiwa yarinyar video ta fada min abinda ya tayar min da hankalina matuka.
Ashe Wanda Ake Zargi ya dade da yiwa yarinyar Lalata, kuma tun tana Shekara 8 yake mata mummunar aika aika da farji da kuma ta dubura ( wa'iyazubillah), da kuma zubar da kazantarsa a bakinta da tilasata mata hadiyewa.
Ashe ya jima yana yi mata barazana idan har ta sake ta fadawa iyayenta zai kashe ta tare da gana mata azaba.
Ashe Makwabta ne da yarinyar Kuma iyayen basu da karfi, akan case din nema har Allah Ya yiwa mahaifinta rasuwa, har ya saka Mahaifiyar yarinyar zuwa Asibitin murtala dake Kano
Yarinyar Har yanzu ko kwanciya bata iyayi saboda zafin ciwon, sai dai ta dan ajiye kanta a kafadar uwarta ta samu ta dan huta, kullun suna cikin zullumi basu da wanda zai taimake su.
Sai da Allah ya kawo Baiwar Allah Shafa’atu Muhammad Adam ta Dauki video ta saka a shafinta har aka dinga taggin namu ni da Abba Hikima da wasu masu Fafutuka.
Likitocin da suka dubu yarinyar suka ce, tunda suke basu taba ganin lalata da illa irin yadda aka yiwa wannan baiwar Allah ba. Suka ce ko da ma ta samu Sauki zaiyyi wuya ta samu haihuwa ko juna biyu saboda abun ya taba mata Mahaifa da hanjinta.
A Yanzu dai Mai Girma Gwaman Jahar Jigawa tare da mai Dakinsa sun aika da tawaga zuwa Asibitin murtala har ma an turata zuwa Mal Aminu Kano Kano Teaching Hospital don yi mata aiki tare da Jagoranci Dr Hauwa Babura wanda muka magantu da ita sosai
Insha Allah Zamu bibiyi wannan case din nida Abokina Abba Hikim, Insha Allah sai mun tabbatar da anyi mata adalci