Ba duk maza bane suke tsufa da lafiya da kuma karfin azzakarin su ba. Wasu ma tun daga samar ta kansu suke da raunin gaba. Masu matukar sa'a sune wadanda idan shekaru sun soma ja a wannan lokacin ne gabansu ke sakewa na rashin karfi.
Akwai wadanda Allah Ya musu baiwar lafiyar azzakari ba tare da sun sha magunguna ba. Daga yarintarsu zuwa tsufansu duk cikin kuzari suke.
Shi kansa azzakari tamkar injin mota yake. Yana bukatar kulawa na musamman domin ganin namiji ya samu damar tsufa da lafiyar gabasa. Baya ga abinci da kuma abubuwan sha da ya kamata maza su rika kulawa wajen cin su saboda yadda suke jawo raunin gaba. Da akwai kuma wasu hanyoyin guda 7da ya kamata duk namiji ya rika kula dasu domin gyaran gabansa muddin yana son ya rika cin gaban matarsa.
1: Tsafta cewa: Ya zama dole a duk kullum namiji ya tsaftace gabansa A kalla sau uku a rana da ruwan ɗumi.
Zaka tabbatar ka wanke azzkarinka zuwa ƙasan marainanka. Duk wajen da yake da gashi ka tabbatar la tsaftace shi yadda babu wani ɗauɗa ko ƙazantar da zai samu wajen ɓuya.
2:Aski : Barin yawan gashin gaba yana iya baiwa cututuka damar shiga jikin namiji harma ya shafi matarsa.
Sai sayi ko kuma tal kobo shine abunda yafi dacewa da gashin gaban kowani namiji domin samar da lafiyar azzakarin sa. Idan gashi yayi yawa duk yadda akayi ƙoƙarin tsaftace shi dole sai datti ya samu mafaka.
3: Kula da Ƙananan Ƙuraje: Duk yadda kaga wani kurji ya fito maka a gaban ka kada kayi gaggawar kace zaka matsa shi. Kayi kokarin samun maganin kashe kuraje ta hanyar ganin likitan ka.
Maza da dama sun gabansu ya samu lahani ne wajen sakaci da irin haka.
4:Tsaftace Kamfe : Akwai wasu mazan da sai suyi kwana da kwanaki suna maimaita saka Kamfe guda daya ajikinsu kuma ba tare da sun tsaftace shi ba. Wanda hakan yana jawo cuta ya shiga gaban namiji. Don haka tsaftace wandon ciki yanada mahimmanci.
5:Kula Da Abinci : Zaki da yawan cin maiko yakan jawo raunin gaba. Don haka kula da abinci da kuma kayan shaye shayen da maza ke amfani dasu suna da tasiri ga lafiyar mazakutarsu.
Haka kuma duk wani abinci mai wari ko yami barasa da kuma shan taba sigari suna da yiwa azzakari illa kamar yadda masana suka tabbatar.
Irinsu albasa da tafarnuwa abinci ne da suke fita a gaban namiji idan yayi amfani dasu kamin jima'i.
6:Shafe shafe: Wasu maza suna yiwa azzakarin su shafe shafe. Ta fashe feshen foda da turarufukan da sukan iya musu illa a gabansu.
Shi azzakari ba fuskar mace bane da za a masa irin wadannan shafe shafe. Don haka sai a kiyaye.