ALLAHU AKBAR; Allah Kasa Mudace Duniya Da Lahira Duk Wani Musulmi Sai Yayi Kwanciya Kabari……




ALLAHU AKBAR; Allah Kasa Mudace Duniya Da Lahira Duk Wani Musulmi Sai Yayi Kwanciya Kabari……

DUK WANDA YA RUFE GAWA BA TARE DA YA YI MATA RIJISTA BA, ZAI BIYA TARAR NAIRA DUBU 50,000 KO YA FUSKANCI GIDAN KASO– Majalisar Kaduna

Muhammad Malumfashi Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kawo wani kudiri da zai kawo gyara wajen harkar bizne mamata a fadin jihar.

Wannan kudiri zai sa a rika yi wa kowace gawa rajista kafin a bizne ta a cikin makabarta.

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, wannan kudiri da majalisar jihar ta kawo, za ta bada dama ga kananan hukumomi su karbe makabartun jihar sannan su rika bada satifiket na bizne mamacin a duk lokacin da aka rasu.

Mataimakin shugaban majalisar dokoki na jihar Kaduna, Nuhu Shadalafiya, shi ne ya jagoranci wannan zama a da aka yi a Ranar Alhamis 18 ga Watan Afrilu, inda mafi yawan ‘yan majalisar jihar su ka amince da wannan kudiri.

Honarabul Shadalafiya yake cewa wannan kudiri idan ya zama dokar jihar, zai ba kananan hukumomin Kaduna ikon ware kudi wajen gina makabartu da katangewa da duk daukar nauyi da kuma kula da batun tsaro da sha’anin ma’aikata.

An amince da wannan kudiri ne bayan kwamitin da yayi wannan aiki ya gabatar da rahotonsa a gaban zauren majalisar.

Kudirin zai haramtawa jama’a bizne mamata a wuraren zaman al’umma. Kuma za a ci tarar wanda ya sabawa dokar.

akbar-allah-kasa-mudace-duniya-da-lahira-duk-wani-musulmi-sai-yayi-kwanciya-kabari ga duk wanda ya sabawa wannan doka ya binze mutum a inda bai dace ba, ko kuma ya rufe gawa a makabarta ba tare da ya samu shaidar rajista daga mahukuntan kananan hukumomi ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post